Majalisar wakilan Najeriya ta sha alwashin sa ido wajen aiwatar da kasafin kudi na 2016

Majalisar wakilan Najeriya ta sha alwashin sa ido don tabbatar da bangaren zartarwa ya aiwatar da kasafin kudi na 2016 dari bisa dari cikin gaskiya da adalci.

Dan majalisar tarayyar mai wakiltar mazabar Yamaltu/Deba a jihar Gombe dake arewa maso gabashin Najeriya, Honabul Abubakar Ahmed Yunusa, shi ne ya bayar tabbacin hakan a yayin zantawarsa da Muryar Najeriya a offishinsa da ke zauren majalisar a Abuja babban birnin kasar.

Honabul Yunusa ya ce ko da yake dai al’ummar Najeriya na ganin an sami tsaiko kafin shugaban kasa ya rattaba hannu akan kasafin kudin na 2016, amma wannan ba wani sabon salo ne ba.

’’Ina so in tabbatar wa da jama’a cewa wannan ba shi ne karo na farko da aka sanya hannu a kan kasafin kudi a watan Mayu ba.
“Tun daga 2008 gwamnatocin da suka wuce musamman ma na 2014 da 2015 duka cikin watan Mayu a ka sa hannun a kan kasafin kudi.
“A cikin shekara ta 2011 ma 27 ga watan Mayu, saura kwana biyu kacal gwamnatin ta cika shekara guda aka rattaba hannu akan kasafin kudi.” In ji Honabul Yunusa

Yace majalisar dokoki ba za ta taba bari a yi facaka da kudaden gwamnati kamar yadda gwamnatocin da suka wuce suka yi a baya ba. A don haka za ta dauki kwararan matakai na ganin cewa ba a yi al’mubazzaranci da dukiyar kasa ba.

“majalisar dokoki ce ta yi kasafin kudi kuma hakkinta ne ta bi kadi domin tabbatar da aiwatar da shi, saboda haka a shirye muke a majalisa. Muna tabbatar wa da ‘yan Najeriya mu wakilansu ne, za kuma mu tsaya mu ga mun tabbatar duk wasu ma’aikatu, da hukumomi da sashe-shashe na gwamnatin tarayya abin da aka kasafta aka bai salwanta ba’’. A cewar honorabul Abubakar Ahmed Yunusa

Ya ce shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sha alwashi sai an aiwatar da kasafin kudi na 2016 da kashi 70 ko 80 cikin 100.

Ya kara da cewa gwamnatocin da suka shude babu wanda ya taba aiwatar da kasafin kudi kusa da kashi 50 cikin 100, amma shugaban Buhari ya yi alkawari, mu kuma a majalisa a shirye mu ke mu mara masa baya don cimma wannan buri.
Za mu tabbatar da cewa ko Kobo bai salwanta ba wajen aiwatar da kasafin kudin.

Kazalika, dan majalisar ya yi kira ga al’ummar Najeriya da ta kara hakuri da juriya duba da irin halin kuncin rayuwa da ake fama da shi a kasar, tare da yin albishir nan ba da jima wa ba al’ummar Najeriya za ta fara kwankwadar romon demokuradiyya karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari.

Abdulkarim Rabiu