MDD ta zargi Kungiyar al-Shabab da Daukan Yara Aikin Soji

Wani babban jamiin asusun tallafa wa yara na Majalisar Dinkin Duniya ko MDD, yace ba za a rasa yara da yawan su yakai 5,000 ba a Somalia wadanda suke cikin sojojin al-Shabab.

 

Sai dai har yanzu ‘yan kungiyar na ci gaba da kamfen dinta na daukan yara matasa aikin soja.

 

A cikin wata hira da yayi da sashen Somaliyanci na gidan Rediyon Muryar Amurka, Susannah Price wadda itacekakakin hukumar ta UNICEF tace ci gaba da daukar matasa da kananan yara aikin soja babban abin damuwa ne, domin tana jin adadin sai kara hauhawa yake yi.

 

Price tace gaskiya wannan abu, abin damuwa ne, domin akwai akalla yara kanana da yawan su yakai dubu 5 a matsayin sojojin wannan kungiyar, kuma dabarar data ke anfani da shi ita ce na jan hankalin yaran tare da lallashin su, wani lokaci ma har sukan basu abinci da kudi.

 

“Yaran da suka fi zamewa cikin wannan hadarin sau tari yaran dake zaune ne a sannanin ‘yan gudun hijira”. In ji Price.

 

Tace a wani lokaci can baya an kiyasta cewa yawan su yana tsakanin dubu 2 zuwa 3 ne, wani lokaci ma zaka taras yaran, har akwai ‘yan shekaru 9 a cikin su.

 

VOA/Abdulkarim Rabiu