Musulman Najeriya sun fara azumin watan Ramadan

A Najeriya, al’ummar Musulmi sun bi sahun Musulmai fiye da Miliyan dubu da dari fiyar dake fadin duniya domin soma azumin watan Ramadan bayan mai alfarma Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubukar, ya bayyana ganin wata ranar Lahadi.

A wata sanarwa Sarkin Musulmi, kuma shugaban Majalisar kula da harkokin Mulunci ta Najeriya Alhaji Sa’ad Abubakar, ya bukaci Musulman kasar su yi amfani da watan mai tsarki wajen yi wa kasar addu’ar hadin kai da ci gaba.

Sarkin Musulmin yace ’’rahotanni masu inganci daga shuwagannin Musulci a ko ina dake fadin kasar sun yi nuni da cewa an ga watan Ramadan a wurare da dama, a don haka ina kira a gareku ku yi amfani da wannan da ma wajen yi wa kasa addu’ar zaman lafiya da ci gaba’’.

kazalika ya yi kira ga Musulman da su tabbata sun zauna da makwaftasu cikin kwanciyar hankali da lumana duk kuwa da irin banbancin addini ko kabilanci dake tsakaninsu.

Ramadan dai wata ne mai alfarma ga musulmi, domin kuwa a cikinsa ne aka saukar da Al Ƙur’ani mai tsarki.

 

 

Abdulkarim Rabiu