Najeriya, Kamaru da MDD sun sanya hannu kan yarjejeniyar dawo da yangudun hijira

Gwamnatin Najeriya ta rattaba hannu akan wata yajejriyaniya ta hadin gwiwa tsakanin majalisar dinkin duniya da janhuriyar kamaru domin dawo da yan gudun hijirar Najeriya gida wadanda yanzu haka suke samun mafaka a kasar Kamaru.

Babban Daraktan hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa a Najeriya (NEMA), Muhammad Sani sidi, ne ya bayyana hakan yayin da wata tawagar taimakon jinkai ta majalisar dinkin duniya karkashin jagorancin Dakta Aisha Laraba Abdullahi kuma kwamishiyar harkokin siyasa ta kungiyar Tarayyar Afrika, ta kai ziyasa a hedikwatar ofishin a ranakun karshen mako.

Ya ce akwai kimanin yan Najeriya 80,000 wadanda suka kauracewa matsugunansu da yanzu haka suke samun mafaka a kasar Kamaru wadanda kuma gwamnatin tarayyar take kokarin samar masu da bukatun yau da kullum.

Kazalika ya bayyana cewar gwamnatin tarayya tare da hadin gwiwar jihohin da rikin Boko Haram ya shafa, da majalisar dinkin duniya da ma wasu kungiyoyin da ba na gwamnati ba,  gami da kamfanoni masu zaman kansu cikin shekaru hudu da suka gabata sun yi iyakar kokarinsu wajen kula da dubban mutane da suka kauracewa matsagunansu a sanadiyyar rikicin Boko Haram a yankin arewa maso gabashin Najeriya, ya kara da cawa “an sami ci gaba ta fannin bayar da agagjin gaggawa ya zuwa matakin dawa da yan gudun hiraya garuruwansu da suka kauracewa”

Har-ila-yau ya bukaci kwamishiyar da ta yi amfani da kyakkyawan ofishinta  amatsayinta na kwamishiniyar kula da harkokin siyasa na kungiyar tarayyar Afrika wajen neman karin taimako da goyon baya don tallafawa al’ummomi da jihohin da alámarin ya shafa.

 

 

 

Abdulkarim Rabiu.