Najeriya ta ware Naira biliyan dari biyar don yaki da talauci

Sanata Ali wakili Sanata mai wakiltar mazabar jihar Bauchi ta kudu kana shugaban kwamitin yaki da talauci da samar da walwala na Majalisar Dattawan Najeriya, ya bayyana cewa an ware Zunzurutun kudi har Naira biliyan dari biyar cikin kasafin kudin bana, domin fatattakar fatara a tsakanin matasan Najeriya.

Sanata Ali wakili yace Gwamnatin tarayyar Najeriya karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari ta kudiri aniyar horas da matasa akalla dubu dari biyar akan aikin koyar wa domin su rinka koyarwa a makarantun kasar.

Gwamnatin kuma zata bada tallafin kudi ga matasa masu sana’oin hannu domin su sake bunkasa sana’oin nasu.

Har-ila-yau,  Malam Ali wakili ya ce suma mata baza a barsu a baya ba domin kuwa  Gwamnatin za ta tallafa masu ta ko wacce hanya kamar yadda aka alkawarta ga matasan wannan kasa.

Ya kara da cewa nan bada jima wa ba za’a kira taron jin ra’ayin jama’a kan wani kudiri da abokin aikin shi daga jihar Sokoto wato Sanata Gobir ya gabatar a majilisar domin samar da wata doka ta kafa hukuma ta musamman domin fatattakar talauci a tsakanin yan kasar.

Da ya juya batun tsaro,  Sanatan mai wakiltar jihar Bauchi ta kudu dake yankin Arewa maso gabashin Najeriya yace  ya zama wajibi ga ‘yan Najeriya su Kara godewa Allah, su kuma godewa shuga Buhari gami da dakarun tsaron Najeriya dangane da mayar da hankali wajen yaki da yan Boko Haram gadan-gadan.

”yanzu haka Musulmai da mabiya addinin kirista na zuwa masallatai da majami’ai ba tare da fargaba ba, amma a can baya ko kasuwa mutum zai shiga yana tattare da zullumi har sai ya ga fitowarsa lafiya.

“Àmma a halin yanzu lamarin ya sha ban-ban domin kuwa zaman lafiya ya dawo yankin kashi casa’in da biyar cikin dari.  Inji Sanata Ali wakili.

Dan gane da batun ziyarce-ziyarce na Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari kuwa, Sanatan wanda har ila yau tsohon jami’in hukumar han fasakauri ta kasa a Najeriya wato Customs a turance, yace abu ne mai kyau kwarai matuka, domin kuwa kowace tafiya da shugaban ke yi tana da manufa lokaci ne kawai ba zai bamu damar lissafa su daki-daki ba.

Amma kowa ya san haka domin kuwa a fili yake baro-baro sai dai kawai san zuciya na wasu yan hana ruwa gudu.

Kadan daga cikinsu akwai kokarin maido da kudin kasa da wasu makiya kasa suka yi awan gaba da su a can baya da kuma maido da martabar Najeriya a idon duniya, gami da kara dankon zumunci tsakanin kasar da sauran kasashen duniya.

A karshe ya yi addu’a Allah ya maido da shugaba Muhammadu Buhari da dukkanin mukkarabansa gida lafiya a taron kasasahe sittin da suke halarta yanzu haka a birnin Burtaniya.

 

 

Abdulkarim Rabiu/Mus