Najeriya ta yi kira da babban murya kan sake farfado da Tafkin Chadi.

Najeriya na daukar matakan da suka wajaba don tabbatar da dawo al’ummarta gida cikin koshin lafiya, wadan da yanzu haka suke zama a matsayin yan gudun hijira a kasashen dake makwaftaka ta ita.

Maitamakin shugaban Najeriya, Farfessa Yemi Osinbajo ne ya bayyana hakan yayin da ya bude taron tattauna agame samar da kariya a Tafkin Chadi wanda ya gudana a Abuja babban birnin Najeriya.

Ya ce abin damuwa ne yadda rikicin Boko Haram ya tilastawa wasu yan kasar tserewa zuwa makwaftan kasar.

Ya ce nan bada jimawa ba labarinsu zai sauya domin kuwa gwamnati zata ci gaba da maida hankali wajen dawo da su gida, yayin da kuma yake mika godiyarsa ga kasashen da suke makwaftaka da Najeriyar.

“a cikin shekaru 7 da suka gabata, yankin Tafkin Chadi ya funkanci masifu iri daban daban, inda daruruwan mutane suka yi gudun hijira domin tsira da ransu daga hannun Yan Boko Haram. Lamarin ya kazanta yadda al’ummar Najeriya ke kwarara zuwa kasashen dake makwataka da ita, da yadda suke bukatar samun kariya da kyakyawar kulawa. Ina mika godiya ta ga kasashen da suke makwaftaka da mu dangane da yanda suka karbi al’ummar Najeriya, suka basu matsuguni da kulawa a kasashensu. Hakika yin hakan ya nuni da cewa kawunanmu a hade suke’’ In ji mataimakin shugaban na Najeriya.

Farfessa Osinbajo ya kuma bayyana damuwarsa danga ne da koma bayan da Tafkin Chadin yake fuskanta, yayin da kuma  ya bayyana mahimancinsa ga kasashen da suke kewaye da shi.

‘’a ko da yaushe Tafkin Chadi wuri ne na kyakkyawan fata ga jamaá. Kuma a ko wani lokaci hanyoyin ruwansa da danshin kasa na samar da ruwan sha ga jama’a da dabbobi da kuma kuma noman rani, kana da abinci ga mutane da yawa gami da ayyukan yi ga masunta a kasashe 7 dake suke kewaye da shi. Tafkin shi ne mafi girma a Afrika ta da yafi adana ruwa a yankin Sahel”. A ta bakin Mataimakin shugaban kasar.

ya ce taron yana da matukar mahimmanci ga ci gaban tattalin arzikin kasashen da suka yi iyaka da Tafkin Chadi, adon haka ya bukaci taimakon yan Najeriya da ma kasashen da suke  Makawaftaka ta ita wajen gano bakin zaren kalubalen da al’ummar yankin suke fuskanta.

 

Abdulkarim Rabiu.