NNPC ya saka Naira Biliyan 69 a baitil malin Gwamnatin Tarayya

kamfanin man fetur na kasa a Najeriya (NNPC) ya saka Naira miliyan dubu sittin da tara da miliyan dari biyar da arbaín da hudu a baitil malin gwamnatin tarayyar kasar.

Wannan na kunshe ne a cikin rahoton wata-wata da kanfanin yake fitarwa na watan Maris a garin Abuja.

Rahoton ya bayyana cewa, wannan shi ne ya kai ga addadin Naira Triliyon daya da biliyan dari da goma sha daya, na kudin da kanfanin ya biya a asusun na Gwamnatin tarayyar na kudaden da ake samu ta bangaren danyen mai da iskar gas  daga watan Afrilun 2015 zuwa Maris din 2016.

Ya kara da cewa kamfanin na NNPC ya samu kudaden shiga da suka kai Naira biliyan dari da bakwai da miliyan dari twakwas da ashirin da shida a cikin watan maris din wannan shekarar, a maimakon Naira biliyan dari da hudu da miliyan  dari takwas da hudu a watan Fabrairu.

Har-wa-yau rahoton yace an sami karuwar kudaden da ake samu da kashi biyu da digo tamanin da takwas cikin dari daga Naira biliyan dari da ashirin da tara da miliyan talatin da hudu da a ka samu a watan da ya gabata.

A cewar rahoton kamfanin ya kuma samu faduwa ta naira biliyan goma sha takwas a cikin watan da aka gudanar da sauye-sauye a kamfanin.

Rahoton ya kuma bayyana cewar kamfanin samar da Iskar Gas na Najeriya ya sami ribar Naira biliyan biyar da miliyan dari da hamsin da biyar.

matatar mai ta Kaduna ta sami faduwa ta Naira biliyan daya da miliyan dari takwas da ashirin da hudu sannan Warri kuwa ta sami faduwar Naira biliyan daya da miliyan dari tara da sabaín da daya, yayin da Warri ta sami faduwar Naira Miliyan dari takwas da arbaín da biyar’’. A cewar rahoton

 

Abdulkarim Rabiu