Rundunar sojin Najeriya ta bukaci zaman lafiya a tsakanin alúmma

An buka ci yan Najeriya da su zauna da juna lafiya domin kaucewa tashe-tashen hankula da sunan addini ko kabilanci a kasar.

 

An yi wannan kiran ne a wajen Taron Lakca na shekara-shekara ta sashen kula da harkokin addinin Musulunci na rundunar sojin Najeriya yake shirya wa a ko wane watan Ramadan, da ya gudana, a barikin sojoji na Bonny Camp dake unguwar Victoria Island, a jihar Legos dake kudu maso yammacin Najeriya.

 

Taken taron na bana shi ne ’’ Musulci, da zaman lafiya a zamantakewar alúmma, da kuma kiyaye tashe-tashen hankula’’ Babban bako mai jawabi wanda kuma shi ne kwamishinan harkokin cikin gidan Lagos, Hon. Abdullateef Abdulwaheed, ya bukaci al’ummar Najeriya da ta yi addini da zuciya mai tsarki domin samun zaman lafiya a tsakanin al’umma.

 

Hon. Abdulwaheed ya ce Najeriya kasa ce mai doka da oda, a saboda haka bai kama wani ya kyamaci wani ba, kundin tsarin mulki ya bayar da yancin zaman lafiya a zamantakewar alúmma duk kuwa da irin banbancin addini ko kabilanci dake tsakaninsu.

 

Da yake nasa jawabin darakta kula da harkokin addinin Musulunci na barikin Bonny Camp dake birnin Lagos, kanal Shehu Mustafa, ya ce an zabi wannan taken taro ne bisa wasu hujjoji, kuma ya samo asali ne daga rikicin addini dake faruwa a tsakanin al’ummar Najeriya.

 

Kanal Mustafa ya ce addinin Musulunci addi ne na zaman lafiya, da hadin kai, kuma bai yadda da nuna banbancin kabilaci ko addini ba.

 

Shi ma da yake nasa jawabin babban bako na musmman, Manjo Janar Ismaila Rabiu ya yi kira ga ‘yan Najeriya agame da bukatar dake akwai ta yin hakuri da juna da kuma yin amfani da koyarwar addini, kamar yadda Ubangiji ya umarta da kuma yadda kundin tsarin mulki kasar ya tanadar.

 

Kazalika Janar Rabiu ya yabawa kokarin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na ya samar da zaman lafiya a cikin kasar.

 

Taron lakcar dai ya sami halartar jami’an sojin kasa da na ruwa, da shuwagabannin addi, da babban limamin masallacin rukunin gidaje na 1004, Sulaiman Ibrahim, da Sarkin Hausawa na unguwar idi Araba, da dai sauransu.

 

 

Abdulkarim Rabiu.