Rundunar Sojin Najeriya ta yi wani sunturi na sharar daji a Zamfara.

Tawagar dakaru 223 na rundunar sojin Nageriya ta daya, karkashin shirin SHARAN DAJI sun gudanar da wani sunturi a dajin kauyen Kabaru, a cikin karamar hukumar Maru dake Jihar Zamfara a arewa maso yammacin Najeriya, domin bankado barayin shanu da ‘yan fashi na makami.

A cewar sanarwar Mai Magana da yawun rundunar sojin Najeriya, Kanal Sani Usman Kukasheka ”A lokacin sunturin, sun farwa barayin masu dauke makamai, sannan sun kashe uku daga ciki yayinda wasunsu suka sami raunika’’.

Har-wa-yau dakarun sun gudanar da wani sunturin a dajukan dake kauyukan Kusa, da Bayan Dutse, da kuma Gusami dukkan su a cikin karamar Hukumar Birnin Magaji dake cikin wannan jiha ta Zamfara.

“dakarun sun sami nasasar kwace babura 24, da fankon akwatunan alburusai na musamman 4, da kuma fankon akwatunan alburusai masu tambaya kungiyar tsaro ta NATO 4, sai wayar hannu, da zabba da kuam layu.”

IMG-20160626-WA0013

“ ko da yake dai ba a kashe wani barawo mai dauke da makami ba, amma an yi imani da cewa wasu daga cikinsu sun tsere dauke da raunikan harbin bindiga. An kuma sami nasarar kwato bindiga samfurin AK-47 guda daya, da Ak-47 mai amon wuta, da alburusai, da babura biyu, da shanu guda hudu da suka sace, da kuma adda.

IMG-20160626-WA0014

Dakarun kuma sun sami nasarar kama wani da ake zargin dan aikensu barayin shanun ne a kauyen Gusami.

Daga nan tawagar dakarun ta ci gaba da sunturinta zuwa dajin Maganawa a inda nan ma ta afka wa barayin kana ta kashe daya daga cikinsu kuma ta sami nasarar kwace karamar bindiga guda daya, da alburusai kafin su koma sansaninsu.” A cewar sanarwar

 

Abdulkarim Rabiu