Shugaba Buhari ya bukaci dawo da dukokiyon da aka sace

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yace ba zai bukaci Fira ministan Burtaniya David Cameron ya ne gafara ba bisa kalaman da ya yi kan  cin hanci da rashawa a kasashen Najeriya da Afghanistan ba.

’’ba zan bukaci gafarar daga kowa ba, abin da zan nema shi ne dawo da dukiyoyin da aka sace”

’’ Me zan yi da gafarar Camaron, alokacin da nake bukatar wani abu mai mahimmanci”. In ji shugaba Buhari

Shugaban ya bayyana hakan ne a taron yaki da cin hanki da rashawa da yanzu haka yake gudana a birnin Landan wanda kungiyar kasashen renon ingila ta shirya tare da hadin gwiwar kungiyar tabbatar da gaskiya da adalci ta kasa da kasa.

Shugaba Buhari wanda ya bayyana farin cikinsa da goron gayyatar da aka ba shi a taron, kana ya bayyana cin hanci9da rashawa a a matsayin annoba ko kuma cuta dake addabar ko wace alúmma kama dagaa kasashen da su ka ci gaba ya zuwa wadanda ke tasowa.

’’cin hanci da rashawa babbar bazana  ce ga shugabanci na gari, da bin doka da oda, da zaman lafiya da tsaro da ma shirye-shirye na ci gaba da ake yi da nufin yaki da talauci da farfado da tattalin arziki’’. In ji shugaba Buhari

Kazalika, Shugaba Buhari ya bayyana cewa gwamnatinsa ta nada manyan ajandodi guda uku da zata fi bai wa fifiko, wadanda suka hada da tsaro, yaki ta cin hanki da rashawa da kuma samar da aikin yi ta hanyar farfado da tattalin arziki.

’’ gwamnatinmu ta fara da yaki da cin hanci da rashawa, domin shi ne babbar matsalar da kasar ta ke fuskanta a yanzu ta bangaren alúma da tattalin arziki’’.

’’Muna bukatar kara jajircewa wajen yaki da cin hanci, muna mutukar kokari ta wannan fanni, ta hanyar nuna shugabanci nigari’’. in ji shugaba Buhari

Shugaba Buhari ya bayyana cewa yaki da cin hanki da rashawa yana da mutukar wuya, amma a wurinmu mai yiyuwa ne.

Ya kara da cewa yaki da cin hanci da gwamnati take yi alamu ne na yanci da goyon baya akan hukumomin da suke yaki da taaddanci domin su sami damar gudanar da aikinsu bat are da wani cikas ba.

Kazalika shugaba Buhari ya bayyana cewa Najeriya a shirye take ta rattaba hannu akan yarjejeniyar hadin gwiwa da gwamnatoci akan yaki da cin hanci da rashawa.

 

 

Abdukarim Rabiu