Shugaba Buhari ya dawa gida Najeriya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya dawa a Abuja babban Birnin kasar, bayan ya shafe makwanni biyu a birnin London.

Gwamnan Jihar Kogi yahaya Bello, da takawaransa na Zamfara Abdulaziz Yari ne su ka tarbe shi da misalin 5:30 na yamma agogon Kasar.

Sauran wadanda suka tarbi shugaban kasar a filin sauka da tashin jiragen sama na Nnamdi Azikwe sun hada da sanatoci, da ministoci da manyan hafsoshin rundunar sojin Najeriya.

Kawo yanzu dai shugaba Buhari ya isa gidansa dake fadar shugaban kasa.

Abdulkarim Rabiu