Sojojin Najeriya sun kara tarwatsa sansanonin yan taádda a dajin Sambisa.

Dakarun rundunar sojin Najeriya sun tarwatsa kauyuka hudu a dajin sambisa wadanda suka hada da Bala karega, da Goske, da Harda da kuma Markas.

Dakarun dai sun ci gaba da kai hare-hare a kan ‘yan Boko Haram da har yanzu suke boye a dajin na Sambisa.

A cewar wata sanarwa da ta fito daga ofishin daraktan yada labarai na rundunar sojin Najeriya, kanal kukasheka Usman, “babu dan taádda ko daya a duka kauyukan yayin da yan Boko Haram suka kauracewa matsugunanansu”

“Ko da yake dai an yi wa dakarun kwanton bauna a kauyen Harda, yayin da suke tafiya. Amma duk da haka sojojin sun sami nasarar tarwatsa yan taáddan ba tare da wani daga cikin sojojin ya sami rauni ba”.

“ sojojin sun sami rigunan da suke dauke da bama-bamai da ake kai Karin kunanr bakin wake da su, da muggan makamai da suka hada da bindigogi sanfurin Ak-47 da rokoki da kuma bindigogin masu luguden wuta da batira na hada wutar lantarki mai amfani da hasken rana’’. In ji kanal Usman

Ya kara da cewa dakarun sun sami nasarar kwace motoci guda goma da Babura hamsin mallakar yan taáddan da suka tsere daga matsugunansu.

A wani labarin kuma, an rawaito cewa ‘yan Boko Haram sun yi amfani da damar da suka samu ta ruwan saman da aka tafka domin kara matsawa kusa da in da sojojin suka ja daga.

A cewar sanarwar, ’’dakarun da suke sintirin sun sami nasarar fatattakar ‘yan taáddan da suke kokarin kai wa sojin  hari. kawo yanzu sun kama motoci biyu kuma sun kashe kimanin  yan Boko haram takwas kafin duhuwar dare’’.

’’A kwai yiyuwar gano wasu abubuwan a wayewar garin yau. Za mu ci gaba da sanar da ku yadda aikiin yake wakana’’.

 

Abdulkarim Rabiu