Tawagar AU ta bukaci sasanta rikicin Burundi

Tawagar mambobi 15 na kwamitin sulhu na kungiyar tarayyar Afrika AU ya bukaci gaggauta tattaunawar da zata samar da masalaha a rikicin da aka shafe shekaru da dama ana yi a Burundi, bayan da kwamitin ya kammala ziyar gani da ido ta kwanaki hudu a kasar.

“ cikin kwanaki hudu, mun gana da kungiyoyi da hukumomi daban-daban ciki kuwa harda shugaban kasar Burundi, da kuniyoyin al’umma, da jamian diflomasiyyar majalisar dinkin duniya dake Burundi, da kuma dukkan masu ruwa da tsaki na kasar, kuma sun ce suna so a gaggauta sasanta rikicin,” in ji Lazare Makayat Safouesse shugaban tawagar kwamitin sulhu na Kungiyar tarayyar Afrika.

Ata baikinsa duka kungoyoyin sun bukaci hanzarta tattaunawa domin sasanta rikicin da aka shafe tsawon shekaru ana yi a Burundi.

‘’ tattaunawar cikin gida da ke karewa nan da watanni hudu zata iya share fajen wata sabuwar tattauna a matakin na kasashen waje karkashin jagorancin masu shiga tsakani daga kasashen dake gabashin Afrika, in da shugaban Uganda Yoweri Museveni zai kasance a matsayin babban mai shiga tsakani yayinda tsohon shugaban Tanzaniya Benjamin Mkapa zai kasance mataimakinsa,’’ in ji Safouesse

Har-ila-yau ya yaba da ziyarar da Mkapa ya kai kwananan a birnin Brussels na kasar Belgium a inda ya gana da al’ummar Burundi wadanda basu sami damar halartar tattaunawar sulhu da aka gudanar cikin watan Mayu a birnin Arusha na kasar Tanzania ba.

Shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza ya gana da mambobin tawagar kwamitin sulhu na kungiyar tarayyar Afrika a birnin Makamba dake da nisan kilimita 200 daga Bujunbura babban birnin kasar.

Rikicin siyasa ya barke a kasar Burundi ne a cikin watan Afrilu bayan da shugaban kasar ya bayyana aniyarsa ta sake tsawa takarar shugabancin kasar a karo na uku.

Lamarin day a haifar da zangar-zangar adawa da ta yi sanadiyar tashe-tashen hankula har ma da yunkurin kifar da gwamnatin wanda bai ci nasara ba.

Rahotanni sun yi nuni da cewa fiye da mutane 45 aka kashe yayin da 270,000 suka yi gudun hijira zuwa kashen dake makwaftaka ta kasar ta Burundi.

 

Abdulkarim Rabiu.