Tsawa ta kashe mutum 79 a India

Jami’ai a Indiya sun ce akalla mutane 79 ne suka mutu bayan tsawa ta fada musu a jihohin Bihar da Jharkhand da kuma Madhya Pradesh.

 

Mutane 53 ne suka mutu a jihar Bihar, yayin da mutane 10 suka mutu a a gabashin Jharkhand, sannan mutane 16 suka mutu a Madhya Pradesh.

 

Rahotanni sun ce akasarin mutanen sun mutu ne a lokacin da suke aiki a gonakinsu, yayin da ake tafka ruwan sama.

 

Ana yawan yin tsawa a India lokacin da ake tafka ruwan sama.

 

Alkaluma sun nuna cewa akalla mutane 2,000 ne ke mutuwa a duk shekara sakamakon fadawar da tsawa ta yi musu a India tun daga shekarar 2005.

 

BBC/Abdulkarim Rabiu