Uwargidan shugaban Najeriya ta bukaci gaggamin wayar da kan jama’a akan cutar tarin Fuka.

Uwargidan shugaban Najeriya Aishatu Buhari ta yi kira ga wata kungiyar mai zaman kanta dake rajin yaki da cutar tarin fuka da ake kira Stop Tuberculosis (TB) Partnership Nigeria, da sauran kungiyoyin dake ayyukan ci gaba da su gudanar da gaggamin wayar da kan jama’a don kawo karshen cutar tarin fuka a cikin kasar.

Mai dakin shugaba Buharin ta bayyana damawarta agame da matsayin Najeriya na kasan cewa ta farko a Afrika kuma ta hudu a cikin jerin kasashen ta suka fi kamuwa da cutar a duniya.

Hajiya Aisha Buhari wadda jakada ce ta gaggamin yaki da cutar ta tarin fuka, wato ’Stop TB Campaign a turance’, ta bayyana cewa Najeriya ta sami wannan matsayin ne sabo rashin isasshen bincike akan cutar, idan aka yi la’akari da yadda sauran kasashen duniya ke yi, a dalilin haka ne ma mutane dubu dari shida suke kamuwa da cutar duk shekara, wani a bin ban takaici ma shi ne kashi 60 cikin 100 da suke kamuwa da cutar yara kanana ne.

Uwargidan shugaban kasar wadda ta sami wakilcin mai dakin maitaimakin shugaban kasa Dolapo Osinbajo a taron na kasa da kungiyar ta shirya tare da hadin gwiwar Cibiyar yaki da cutar Tarin fuka da Kuturta ta kasa a Najeriya, ta bayyana cewa daga cikin mutane dubu dari shida da suke  kamuwa da cutar kashi 15 cikin 100 ne kacal suke samun kulawa, yayin da kimanin dubu dari biyar suke mutuwa a dalilin rashin samun kulawa.

Ta ce yayin da gwamnati take kokarin kawo karshen cutar a kwai kuma bukatar kungiyoyi masu zaman kansu da suke ayyukan ci gaba da su bayar da gudunmawarsu.

 

 

Abdulkarim Rabiu.