VON da SEC zasu hada hannu don janyo hankali masu zuba jari

Gidan Radiyon Muryar Najeriya (VON) zai hada hannu da Hukumar kula da harkokin garantin kudi da Musayarsu ta Najeriya (SEC) don tallata kasuwar hannayen jarin kasar.

Babban Daraktan Muryar Najeriya, Mr Osita Okechukwu ne ya bayyana hakan yayin da jami’an gudanarwar Hukumar Musayar hannayen jarin, karkashin jagorancin babban daraktanta Munir Gwarzo suka kawo masa ziyara a ofishinsa dake Abuja Babban birnin Najeriya.

Mr. Okechukwu ya bayyana cewar hadin gwiwar zai taimaka wajen kara amincewar masu zuba jari da kasuwar hada hadar hannayen jari.

’’ga wadanda suke da sha’awar zuba jari, abu na farko da suke so su sani shi ne wani tabbaci kasuwar take da shi? Wannan dangantaka zata taimaka wajen kau da shakku ga martabar Najeriya da kuma fadawa kasashen duniya ana samun sauyin da zai tabbatar da gaskiya da adalci da kuma cancanta,’’ In ji babban dakarn na Muryar Najeriya.

Shima da yake nasa bayanin babban daraktan Hukumar Musayar hannayen jarin, Mr Munir Gwarzo ya ce dangantakar zata taimaka wajen farfado kwarin gwiwar masu zuba jari da bunkasa kasuwar gami da janyo hankalin yan kasuwa daga kasashen ketare.

Ya ce Hukumar Musayar hannayen jari ta fito da wani tsari na tsawon shekaru 10 da zai bunkasa kasuwar hannayen jari ta Njaeriya.

Har-ila-yau ana sa ran tsarin zai taimaka wajen biyan ribar da masu zuba jari suka samu ta Naira Miliyan dubu 80 da har yanzu wasu basu karbi nasu ba.

Da ya bayyana bukatar neman goyan bayan Muryar Najeriya wajen fadakar da jama’a, Gwarzo ya ce tsarin ya kunshi muhimman abubuwa guda dari da daya.

Acewarsa daya daga cikin abubuwan shi ne tsarin biyan ribar da masu hannayen jari suka samu ta asusun ajiyarsu na banki, domin taimaka wa ‘yan kasuwar da suka dade basu karbi tasu ba.

’’ Muna so mu dawo da ‘yan kasuwar da suka gudu, sabuwar dabarar ita ce kada mu bari ‘dan kasuwa ya gudu, ya dawo kasuwa, muna so mu hada hannu domin lalubu bakin zaren kalubalen sabo da mu share fagen bunkasa kasuwar hannayen jarin,” a cewarsa.

Gwarzo ya kara da cewa tsarin zai magance matsalar rashin shigowar masu zuba jari domin adama da su a kasuwar musayar hannayen jarin kafin nan da shekara ta 2025.

 

Abdulkarim Rabiu.