Wakilai 2,873 ne zasu zabi dantakarar APC da zai nemi Gwamnan jihar EDO.

Wakilai dudu biyu da dari takwas da saba’in da uku ne aka tattance da zasu zabi dantakar da jamiyar APC za ta tsayar a takarar kujerar gwamnatin Jihar Edo, a zaben fidda gwani da aka shirya yi a ranar 18 ga watan Yunin 2016.

 

Sakataren gudanar da shirye-shirye na jam’iyyar APC na kasa, Sanata Osita Izunaso ne ya bayyana hakan a sakatariyar Jam’iyyar ta kasa dake Abuja babban birnin kasar, yayin da yake kaddamar da kwamitin zaben mai mambobi bakwai da zasu gudanar da zaben fidda gwani a Jihar Edo.

 

Har-wa-yau an kafa wani kwamitin saurarar kararraki ko da za a samu wasu korafe-korafe bayan kammala zaben.

 

Da yake jawabi bayan kaddamar da kwamitin zaben, shugaban kwamitin zaben, Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, yace kwamitin zai tabbatar da yin gaskiya da adalci akan dukkanin yantakarar.

 

ina so in tabbatar muku cewa za mu yi iyakar kokarinmu wajen yin zaben mai inganci, muna kuma fata ba za a sami korafe-korafe ba. Zamu yi aiki tukuru.  Kuma ina so in yi amfani da wannan damar domin tabbatar da cewa za mu yi wa kowa adalci. Babu wani dantaka da ya banbanta da wani, babu sani ba sabo kuma abin da za muyi a jihar Edo shi ne shi ne muke yi wa APC, da Najeriya da kuma alúmmar jihar Edo’’ In ji Gwamna Masari.

 

Shi ma da yake nasa bayanin, shugaban kwamitin sauraren kararrakin zabe, Mr Opeyemi Bamidele ya  bayyana karfin gwiwar cewa da yardar Allah ba za a sami wasu korafe-korafe ba bayan an kammala zaben fidda gwanin.

 

Yan takara maza 11 da mace 1 ne jimmulla suka bayyana sha’awarsu ta tsayawa takarar kurerar gwamnan Edo karkashin jamiiyar APC. Da suka hada da Mr Blessing Abdulwarith Agbomhre; da Manjo Janar Charls Ehigigie Airhiavbere; Farfessa Fedrick Ebegue Amadasun; Hon. Emmanuel Arigbe Osula: Architect Austin Ilenre Emuan; Kwamared Peter Ekherhalomhen Esele;  sai Barista Kenneth Imansuangbon; Mr Godwin Nogheghase Obaseki, da kuma Rt. Hon. Pius Egberanmwen Odubu; da Mrs Agbarha Aigberadion Osundor.

 

Abdulkarim Rabiu