Gwamnatin Najeriya zata samar da kariya ga masu fallasa kudaden sata

0
8
Minisata watsa labarai Alhaji Lai Muhammad

Gwamnatin Najeriya ta jaddada aniyarta ta bai wa masu tsegunta inda aka boye kudaden sata a kasar cikakkiyar kariya da tukuici, a ci gaba da kokarin da ta ke yi na yaki da matsalar cin hanci da rashawa.

Ministan Watsa Labarai da Raya Al’adu na kasar, Alhaji Lai Mohammed, wanda ya bayyana hakan ya kara da cewa gwamnatin tarayya zata boye sirrin masu fallasa wadan da suka yi sama da fadi da kudaden sata, in ma a bangaren gwamnati ko kuma bangarori masu zaman kansu, kana za a boye sirrin bayanan da suka bayar.

Gwamnatin ta ce kara bai wa ‘yan kasar tabbacin kariyar ya zamo wajibi saboda da fargabar da wasu ke nunawa cewa idan suka fallasa manyan barayi na gwamnati ko na kamfanonimasu zaman kansu, ba za  su samu kariya daga cin zarafi na manyan mutanen da suka fallasa ba.

A kwanakin baya ne dai gwamnatin ta Najeriya ta bullo da wata dabara ta yaki da cin hanci da rashawa, inda ta yi alkawarin bai wa duk wanda ya fallasa inda aka boye dukiyar sata wani tukwici daga cikin abin da aka kwato na kudaden, lamarin da ya kai ga gwamnatin kasar ta samu gano makudadan kudade da aka boye, wadanda ake zargin na sata ne.

Ministan Watsa Labarai da Raya Al’adu na kasar, Alhaji Lai Mohammed, ya ce Kwamitin Karbo Dukiyar Gwamnati na Fadar Shugaban Kasa, ya samu bayanai daga daidaikun ‘yan Najeriya da kungiyoyi wadanda suka nuna fargaba kan tsaron lafiyar masu fallasa wadanda ake zargin manyan barayi ne da suka sace dukiyar gwamnati suka boye.

‘’Masu fallasa wadan da suka yi sama da fadi da dukiyar gwamnati kada su ji tsoron komai domin kwamitin da aka kafa don bayar da kariya, ya kammala shirye-shiryensa na daukar matakan da suka wajaba domin bayar da kariya ga wadan da suka samar da mahimman bayanai, a taikace ma dai masu fallasa manyan barayin basu da asarar komai sai dai ma samun riba’’ in Ministan.

Minista Lai Mohammed ya ce wanda ya fallasa inda aka boye kudin da ya kai Naira biliyan daya, to za a ba shi kashi biyar cikin dari na kudin. Wanda ya fallasa kudin da suka fi Naira biliyan daya kuma, za a ba shi kashi biyar cikin dari na Naira biliyan dayar, sannan kuma a ba shi kashi hudu cikin dari na sauran kudin da suka zarta Naira biliyan daya.

A cewar Alhaji Lai Mohammed, idan kudin da aka gano kuma sun wuce Naira biliyan biyar, to za a bai wa wanda ya tsegunta maboyar kudin kashi biyu da rabi cikin dari na kudin, bayan an ba shi kashi biyar cikin dari na Naira biliyan daya ta farko, da kuma kashi hudu cikin dari na Naira biliyan hudu.

 

 

Abdulkarim Rabiu.

SHARE

bar sako